Ibrahim A. Makama.
Shugaban Darul Al-khair Foundation, Amb. Dahir Abdulrahim, ya ja hankalin matasa kan bukatar su fahimci mahimmancin jagoranci (leadership) da hangen nesa (vision), yana mai cewa da yawan mutane na rasa wadannan abubuwa ne saboda sakaci da rashin tsara rayuwa.
Ya bayyana cewa matasa a kullum suna kokawa da rashin samun dama, amma kuma da yawa daga cikin su ke samun damar amma su saketa su watsar.
Ambassador Ya kara da cewa duk lokacin da matsala tazo, wata dama ce ke tattare da ita, don haka idan mutum ya warware matsalar da ta bijiro masa, zai samu farin ciki da ci gaba.
A cewar sa, idan mutum ko kungiya bata da jagoranci da hangen nesa, ba za su iya tafiyar da komai daidai ba. Saboda haka, yana amfani da wannan dama don tabbatar da cewa Darul Al-khair Foundation na kokarin gano matsaloli da iya warware su domin ci gaba.
Dahir ya kara da cewa “Ni kaina kullum ina zaune ina nazari kan irin matsalolin da za su iya kunno kai a aiki na ko a kungiya ta, sannan nakan duba hanyoyin da zan bi don gyara su da fitar da nemo mafita. Wannan shi ne babban sirrin samun damar ci gaba,” in ji Amb. Dahir Abdulrahim.
Leave a Reply