SIYASA: Gwamnoni na kokarin sauya sunayen wadanda za su samu tallafin kudaden gwamnatin tarayya …

SALEH HUSSAINI TAKAI.

Ministan jinkai Nentawe Yilwatda ya yi zargin cewar yanzu haka gwamnonin jihohi suna can suna kokarin sauya sunayen talakawan da gwamnatin tarayya ke shirin rabawa kudaden tallafi domin rage musu radadin rayuwa. Ministan ya bayyana cewar gwamnonin sun tashi tsaye domin ganin an kauce hanya wajen sanya mutanen da zasu amfana da kudaden saboda dalilan siyasa. Yilwatda ya bayyana cewar suna wannan aikin raba tallafin ne tare da Bankin duniya da kuma wasu kungiyoyin fararen hula domin tabbatar da ganin anyi gaskiya cikin lamarin. Saboda haka ministan yace ko da sunan wasa ba zasu kauce hanya ba wajen tabbatar da cewar kudaden sun kai wa wadanda ake yi domin su. Yilwatda ya ce za’a yi amfani da shaidar ‘dan kasa ta NIN da kuma na banki wato BVN wajen tantance wadanda za su ci gajiyar shirin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *