Khadija Nasir Ziyara.
Gwamnan Jihar Kogi Ahmed Usman Ododo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bada fifiko matuka wajen kulawa da ilimin yara marayu da wadanda basu da galihu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da bikin bude tsarin Gwamna Ododo na kulawa da ‘yan makaranata marayu, lamarin da wani tsari ne da kungiyar mataimaka na musamman na Kananan Hukumomin Jihar Kogi, ya jaddada babu wani yaron da za a watsi da shi ko a manta shi, sanadiyar mutuwar masu kulawa da shi daga Iyaye ko kuma Dangi saboda rashin kudi.
Gwamna Ododo ya jinjinawa kungiyar ta mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi na musamman kan kudurin da suka dauka na taimakon wadanda basu da masu taimaka masu. Ya ce shi tsari wata manuniya ce ga tsarin nasarar gwamnatin sa wadda za ta kai ci gaba ga mutanen Karkara.
Leave a Reply