Ibrahim A makama.
Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da shirin ta na mayar da koyar da harshen Igbo a matsayin dole a dukkan makarantun jihar. Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na kare harshe Igbo da al’adun mutanen Igbo tare da tabbatar da cewa matasa sun san tarihinsu da asalin su.
Gwamnan Jihar Abia, yayin da yake bayyana wannan sabon tsari, ya ce yana da matukar muhimmanci a bunkasa harshen Igbo domin gudun kada ya gushe daga zukatan matasa. Ya kara da cewa koyar da harshen zai taimaka wajen karfafa al’adu da kuma dankon zumunci a tsakanin al’ummar Igbo.
Matakin ya samu karbuwa daga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da al’umma baki daya, inda suka yaba da kokarin gwamnati wajen kare harshen da al’adun da ke da muhimmanci ga ci gaban al’umma.
Wannan tsari zai fara aiki daga matakin firamare har zuwa sakandare, inda za a sanya koyar da harshen Igbo cikin jadawalin karatu na dindindin. Ana sa ran wannan zai karfafa sha’awar matasa wajen jin dadin koyon harshensu na asali tare da girmama al’adunsu.
Leave a Reply