Hassan Turaki.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana dalilin da ya sanya gwamnatin jihar ta yanke shawarar tattaunawa da ƴan bindiga, yace, hakan yafi dacewa kan ayi ta asarar rayukan al’ummar jihar da basu ji ba kuma basu gani ba.
A cewar gwamnan, iyalan wadanda abin ya shafa ne kawai zasu fi fahimtar matakin yadda ya kamata har ma suyi godiya kan dalilin da yasa gwamnati ta dauki wannan mataki mai muhimmanci.
Uba sani ya kara da cewa, “Mutanen da lamarin ta’addancin ya shafa sun yi kira ga a yi sulhun. A misali, Sarkin Birnin Gwari ya yi kira da irin wannan sulhun.
Leave a Reply