JIGAWA: Sanata Babangida ya bayyana cewa zai cigaba da …

Ibrahim A. Makaman.

A wani ƙoƙarin sa na inganta rayuwar matasa da samar da aikin yi a faɗin jihar Jigawa, Sanata Bababgida Hussaini mai wakiltar Jigawa North West ya halarci taron yaye ɗaliban da ya ɗauki nauyin basu horo na musammam a sana’ar hannu ta Fata da suka haɗa da ɗinkin takalma da jaka wanda ya gudana a Cibiyar Koyar da aikin Fata da Kimiyya da Fasaha ta Najeriya (Nigerian Institute of Leather and Science Technology).

A yayin yaye ɗaliban, Sanata Babangida ya gwangwaje ɗaliban da sabon keken ɗinki na zamani da kayan aiki da suka kai Naira Miliyan 3, tare da basu ƙarin Naira Dubu 100 domin ƙara ƙarfafa musu.

Wannan ya zo me mako guda bayan gudanar da aikin ido kyauta da Sanatan ya dauki nauyi a shiyyar Jigawa North West don sauƙaƙawa masu ƙaramin ƙarfi da ke fama da matsalar lalurar ido a yankin.

Sanata Babangida ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukan raya al’umma har sai Jigawa da yi fice tsakanin takwarorin ta wajen cigaba ta kowanne fanni.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *