JIGAWA: Gobarar tankar mai ya sake afkuwa …

Hassan Turaki.
An samu wani gobarar tanka dauke da fetur a wani gidan mai me suna Shakkato filling Station a birnin dutse ta jihar Jigawa.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Lawan Shi’isu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zan yawa da manema labarai a birnin dutse.
Shi’isu yace lamarin ya faru ne yayin da wata tanka dauke da man fetur take sauke mai zuwa tankin dake ajiyar mai na kasa a gidan mai me suna Shakkato dake kan hanyar koyawa inda wutar ta tashi kuma tafi Æ™arfin duk na’urorin dake gidan”
Ya kara da cewa an shawo kan al’amarin ne ta hanyar hadakar ma’aikatun kashe gobara na kasa da na jiha dama temakon gaggawa da jama’a suka bayar, a yayin da ake kashe gobarar jami’an yan sanda hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sunyi wa gurin kawanya domin hana bata gari amfani da wannan dama wajen kwasar dukiyar da ba tasu ba.
Bincike ya tabbatar da cewa ba’a rasa rayuka ba amma har ya zuwa wannan lokaci ba’a tabbatar da alkaluman abubuwan da suka kone ba.
Idan ba’a manta ba a baya an samu rasa rayuka sakamakon gobarar tankar mai a jihar har ma aka rasa rayuka.